29 Satumba 2025 - 08:58
Source: Quds
Yaman Ta Harba Makami Mai Linzami A Filin Jirgin Sama Na Ben Gurion

Harba Makamin ya sanya kunna karar kararrawa a yankuna da dama a Isra'ila. Tare da kawo cikas a filin jirgin sama na Ben Gurion

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da harba makami mai linzami daga kasar Yaman tare da yin ikirarin cewa na’urorin tsaron gwamnatin kasar sun kakkabo shi. Kamar yadda Tashar talabijin ta Channel 12 ta gwamnatin Isra'ila ta kuma yi ikirarin cewa sun yi nasarar kakkabo makamin.

Harba Makamin ya sanya kunna karar kararrawa a yankuna da dama a Isra'ila. Tare da kawo cikas a filin jirgin sama na Ben Gurion.

Your Comment

You are replying to: .
captcha